Labaran tattalin arzikin Najeriya
Gwamnatin Bola Tinubu ta kaddamar da sabon tsarin haraji da zai fara aiki 1 ga Janairu 2026, don rage wa matasa da kananan ‘yan kasuwa nauyi wajen biyan haraji.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin kin sayen matataun man Najeriya. Ya ce akwai kungiyoyi da masu kudi da ya kamata su saye matatun NNPLC a Najeriya.
Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da saka harajin 15% kan shigo da man fetur da dizil daga ketare. Ana hasashen hakan zai iya kara kudin mai.
Masana hada-hadar kudi daga Quartus Economics sun nemi babban bankin Najeriya na CBN da ya kawo sababbin takardun kudi na N10,000 da N20,000 guda daya.
Majalisar Wakilan Tarayya ta kammala tattaunawa kan bukatar ciyo bashin Dala biliyan 2.3 daga kasashen ketare, ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Tinubu.
A labarin nan, za a ji cewa rufe matatar tace danyen mai da dangoginsa da ke Fatakwal ya jawowa kasar asarar makudan kudi da ya kai Naira biliyan 366.2.
Rahoton BudgIT ya nuna jihohi 35 sun tara ₦17.2 tiriliyan a shekarar 2024, amma yawancinsu na dogaro ne sosai da kudaden FAAC daga gwamnatin tarayya.
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta rika ciwo bashi ba bayan cire tallafin man fetur da ya yi a Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar fadada shirin raba tallafin kudi kai tsaye ga 'yan kasa zuwa kananan hukumomi 774. Ministan kudi, Wale Edun ne ya fadi haka
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari