
Labaran tattalin arzikin Najeriya







Bankin duniya ya amince da ba gwamnatin Najeriya bashin kudi har dala miliyan 500 domin habaka tattali. Za a raba kudin ne wa 'yan kasuwa da gidajen jama'a.

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya fadi yadda ya yi barazanar korar Minista Nyesom Wike idan manufofinsa ba su dace da bukatun jam’iyyar APC mai mulki ba.

Minista Wike ya raba buhunan shinkafa 10,000 ga addinai da makarantu a Abuja don Ramadan, inda shugabanni suka gode, suna cewa zai taimakawa mabukata.

Tsohon minista a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya gargadi shugabanni daga kan kansiloli har shugaban kasa da su tabbata sun yi adalci ga al'ummar da suke mulka.

Kunguyar CDD ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Zamfara saboda dalilan karya doka da tattalin arziki.

NAFDAC ta kama buhuna 120 na jabun shinkafa a Rivers, inda ta kai su ofishinta na Kudu maso Kudu, ta kuma kama wata mata tare da kayan hada jabun shinkafar.

Kasuwar hada-hadar ta NGX ta fuskanci koma baya, inda masu hannun jari suka tafka asarar N1.4tn. Duk da haka, masana na ganin dama ce ta sayen hannun jari da araha.

Shirin koyon sana’o’in Gwamnatin Adamawa zai taimaka wa matasa su samu ƙwarewa a fannoni daban-daban, rage rashin aikin yi, da ƙarfafa dogaro da kai.

Tun bayan hukuncin kotun koli kan yancin kananan hukumomi, Gwamnoni na ƙoƙarin hana aiwatar da matakin cin gashin kai da biyansu kudadensu kai tsaye.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari