
Gasar kwallo







Real Madrid ta kasar Spain za ta kece da Borussia Dortmund ta kasar Jamus a wasan karshe na ɓa neman cin gasar kofin zakarun Turai (UCL) 2024 a Wembley.

Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al Nassr ta sha kashi a hannun Al Hilal a bugun fanariti a wasan karshe na gasar cin kofin sarki a ranar Juma'a.

Najeriya ta fuskanci koma baya yayin da tauraron dan wasanta Victor Osimhen ba zai taka leda a wasanni biyu na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026 ba.

Sakamakon kamfanin INEOS ne ya mallaki Manchester United da kuma kungiyar Nice, ana fargabar daya daga cikin kungiyoyin ba zai buga gasar Europa a kaka mai zuwa ba.

Barcelona ta sallami Xavi, yayin da Hansi Flick ke shirin karbar mukamin. An yi tunanin za a tattauna makomar Xavi bayan wasan karshe na Barca a ranar Lahadi.

Fitaccen dan wasan Real Madrid, Toni Kroos, zai cika burinsa na yin ritaya daga buga kwallon kafa a lokacin da ya ke matakin kololuwar ganiyarsa.

Man City ta lashe kofin gasar Premier ta bana bayan da Phil Foden ya zura wallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya a wasan da ta buga yau.

Cristiano Ronaldo ya zama kan gaba a jerin ‘yan wasan da ke karbar albashi mafi tsoka a 2024, wanda shi ne karo na hudu da ya ke jan ragamar, in ji mujallar Forbes.

Kungiyar Real Madrid ta samu nasarar doke Cadiz da ci 3-0 wanda ya ba ta nasarar lashe kofin La Liga bayan ita ma Barcalona ta sha kashi a hannun Girona.
Gasar kwallo
Samu kari