Hukumar Kwastam
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a sansanin jami'an hukumar kwastam a jihar Kebbi. Sun hallaka jami'i daya tare da sace wani jami'in.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta yi asarar daya daga cikin jami'anta a jihar Jigawa. Jami'in ya rasa ransa ne bayan wani dan fasa kwauri ya buge shi da mota.
A lokacin da 'yan Najeriya ke fama da dawowar layukan mai, hukumar kwastam ta cafke wasu dauke da fetur da za a yi safararsa zuwa kasar Kamaru ta iyakar kasar nan.
Kungiyar 'yan kasuwa ta kasa (NHTUN) sun bayyana ra'ayinsu kan janye harajin wasu nau'in kayan abinci da za a shigo da su kasar nan da gwamnati ta yi.
Hukumar kwastam ta kama magunguna da naman kaji na makudan kudi ana shirin shigowa da su Najeriya a jihar Legas. Babatunde Olomu ne ya bayyana haka.
Mai kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabi'u ya kaddamar da gina katafaren asibitin zamani kyauta ga hukumar kwastam a jihar Bauchi. An fara aiki a jiya Litinin.
Hukumar kwastam ta sanar da kama makamai da ake kokarin shigowa da su Najeriya a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke birnin Legas a ranar Laraba.
Hukumar kwastam ta kama makamai da dama a lokacin da ake kokarin shigowa da su Najeriya ta bayan fage domin aikata ayyukan barna da ta'addanci a garuruwa.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta tabbatar da kama makamai da miyagun ƙwayoyi masu jimillar darajar biliyan 4 a tashar jirgin ruwa dake Onne a jihar Ribas.
Hukumar Kwastam
Samu kari