Hukumar NEMA
A labarin nan, za a ji yadda ruwa kamar da bakin kwarya a jihar Kaduna ya jefa bayin Allah a cikin wahala saboda rushewar muhallansu a sassa da dama.
Mummunar ambaliya ta mamaye kauyuka bakwai a Taraba bayan saukar ruwan sama mai yawa, inda kogin Benue ya yi ambaliya tare da lalata gidaje da gonaki.
Hukumar NEMA ta kai agajin gaggawa jihar Adamawa bayan ruwa ya jawo ambaliya a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa. Gidaje da gonaki sun lalace.
Gwamnatin Najeriya ta samo tallafin Dala miliyan 1 daga kasar China domin raba wa jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa a Arewacin Najeriya a damunar bana.
Gwamnatin tarayya ta ce akwai yiwuwar mummunar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa tara. Ta bayyana cewa ambaliyar ruwan da ake hasashe za ta shafi yankuna 14.
Ma’aikatar muhalli ta yi hasashen ambaliya a jihohi bakwai da garuruwa 25, inda NEMA ta umurci mazauna bakin kogin Neja da su gaggauta barin yankunansu.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta bukaci mutanen da ke jihohin Kebbi, Kwara, Neja da ke kusa da kogin Niger su fara shirin kaura saboda fargabar ambaliya.
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 171 a Gombe, ta kashe mutane 4; SEMA ta bukaci mutane su kauracewa sare itatuwa ko zubar da shara a magudanun ruwa.
Benue na fuskantar hare-haren 'yan bindiga; sama da 100 sun mutu, dubbai sun rasa matsuguni. NEMA na neman agaji yayin da aka kafa sansanin 'yan gudun hijira.
Hukumar NEMA
Samu kari