Nadin Sarauta
Mai martaba sarkin Tikau da ke jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema ya riga mi gidan gaskiya a asibitin kwararru da ke garin Potiskum.
Shugaba Bola Tinubu ya karrama Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona da lambar girmamawa ta 'Grand Commander of Order of Nigeria', a yayin da ya cika shekara 90.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a jihar Ebonyi cikin dare. Miyagun sun hallaka babban basarake a yayin harin.
'Yan bindiga sun saki bidiyon mutanen da suka yi garkuwa da su a Zamfara da kewaye, ciki har da wani Alhaji Buhari wanda ya ce shi ne Shamakin Sarkin Zamfara.
Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi ya tafka babban rashin ɗansa na farko, Shehu Mustapha Umar El-Kanemi wanda ya rasu a daren jiya Asabar.
Gwamnatin jihar Sakkwato ta sanar da sauke hakimai goma sha biyar. Ta na zargin wasun su da tallafawa rashin tsaro, rashin biyayya da cinye filin jama'a
Tsohon Sarkin Damaturu na farko, Alhaji Mai Aliyu Muhammad Biriri ya riga mu gidan gaskiya a kasar Saudiyya ya na da shekaru 82 a duniya bayan fama da jinya.
Kwanaki kadan bayan mutuwar Walin Zazzau, Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya nada ɗansa, Abdullahi Nuhu Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau a jihar Kaduna.
A wata sanarwa da masarautar Zazzau ta fitar, ta ce marigayi Marigayi Injiniya Umar ya halarci bikin Hawan Daushe da halartar bukukuwan Sallah kafin rasuwarsa.
Nadin Sarauta
Samu kari