Nadin Sarauta
Babbar kotun jihar Kano ta zaɓi ranar 10 ga watan Oktoba, 2024 domin yanke hukunci a shari'ar da aka nemi hana Aminu Ado Bayero gyara ƙaramar fadar Nasarawa.
Gwamnatin jihar Bauchi ta ware kudi domin gyara tare da inganta fadojojin sarakunan gundumomi 11 na karamar hukumar Dass da ke a jihar. Mun zanta da Muslim Dabo.
Dattawa da shugabannin yankin Okpella da ke jihar Edo sun yi fatali na nadin Lukman Akemokhue a matsayin sarki da Gwamna Godwin Obaseki ya yi a jihar.
Muhammadu Sanusi II zai canza sarautar mutane da yawa a Kano. Bashir Ado Bayero da Bello Ado Bayero za su zama ‘Dan Isa da ‘Dan Lawan Kano a sauye-sauyen.
Ana yin bikin Sallar Gani ne a masarautar Gumel a tsawon kwanaki uku a lokacin Maulidi. Ana Sallar Gani a Daura da Hadeja sai dai akwai banbanci tsakaninsu da Gumel.
Ana zargin wani basarake a jihar Enugu da yin garkuwa da wani matashi mai suna Michael Njoku tare da karbar N2.5m daga iyalansa inda har yanzu bai fito ba.
Yayin da ake ta shirin gudanar da zaben jihar Edo, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole ya roki basarake a jihar kan kura-kurai da ya tafka lokacin yana gwamna.
Mai martaba sarkin Osun, Oba Gabriel Adekunle Aromolan ya rasu bayan jinya da ya yi. Oba Gabriel Adekunle Aromolan ya shafe shekaru 42 a kan karaga.
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya aika da sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar kasar Ijesha da ke jihar Osun bisa rasuwar sarkinsu, Oba Aromolaran.
Nadin Sarauta
Samu kari