Nadin Sarauta
Masarautar Kano ta sanya gwajin ƙwayoyi a matsayin sharadi ga masu neman hawa kujerar sarauta, yayin da NDLEA ta buƙaci al’umma su taimaka wajen yaƙi da shaye-shaye.
Hakimin Gorau ya bayyana yadda ya tsira daga hatsarin kwale-kwale a Sokoto, inda aka binne mutane 62 bayan hatsarin da ya yi sanadin mutuwar fasinjoji da dama.
Sarkin yankin Iyin-Ekiti ya nemi kujerar da Gwamna Biodun Oyebanji ya zauna a kai, amma Cocin Anglican ta ki mika ta saboda an hade ta da kayan bagadi.
Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya amince da kafa sabon gunduma mai kauyuka takwas a Dandi tare da nada sabbin shugabannin gargajiya da za su yi jagoranci.
An karrama tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da sarautar Jigon Bauchi saboda gudunmawarsa ga dimokuraɗiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Gwamnatin jihar Gombe ta fara shirin sake gina Fadar Sarkin Gombe domin kare tarihi da al'adu, ƙarfafa martabar masarautar da tallafa wa zaman lafiya.
Ooni na Ife ya tallafa wa cibiyar tsaron Iru Ekun ta Sunday Igboho da Naira miliyan 100 da motar Hilux, tare da kira ga Yarbawa su hada kai wajen inganta tsaro.
Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya ƙirƙiri sabuwar gunduma a Suru tare da ɗaga Mai Unguwar Tarasa zuwa hakimi domin ƙarfafa tsarin masarautun gargajiya a jihar.
Sarkin Ibadan, Mai Martaba Rashidi Ladoja ya yabawa Tinubu kan yaƙi da satar mutane, yana cewa kin biyan kuɗin fansa ta taimaka wajen ceto mutanen Oyo lafiya.
Nadin Sarauta
Samu kari