Musulmai
A labarin nan, za a ji yadda gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana kokarin ganin jama'a sun rayu a cikin walwala, yayin da ta ba da hutun Sallah babba.
Sarkin Epe da ke jihar Legas a Kudu maso Yammacin Najeriya, Shefiu Ọlatunji Adewale ya kwanta dama yana da shekara 86, za a yi janazarsa yau Asabar.
A 2025, babbar sallah (Eid Al Adha) za ta kama ranar 6 ko 7 ga Yuni, kamar yadda aka sanar. Kasashe 5 da suka hada da Pakistan da India za su yi sallah a 7 ga wata.
Gidauniya daga ƙasar Turkiyya za ta yi layyar shanu 6,000, sannan ta raba wa musulmi naman a Abuja da wasu jihohi 11 ciki har da Kano da Kaduna da babbar sallah.
An bayyana muhimman ayyukan ibada guda 10 da ke so kowane Musulmi ya yi a kwanaki 10 na farkon watan Zul Hijja. Ana son yin azumi a ranar Arafah.
Wata mahajjaciya daga jihar Filato, Hajiya Zainab ta nuna halin gaskiya da riƙon amana yayin aikin hajjin 2025, ta mayar da $5000 da ta tsinta ga mai su ɗan Rasha.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar II ya bayyana gobe Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1446H.
Hukumomin ƙasar Saudiyya su sanar da ganin jinjirin watan Babbar Sallah yau Talata, sun ce alhazai za su yi hawan Arfah ranar Alhamis, sallah ranar Juma'a.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a matsayin limamin Arafa da zai yi huduba wa miliyoyin musulman duniya a Namira.
Musulmai
Samu kari