Masu Garkuwa Da Mutane
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Malumfashi, Kurfi da Dutsinma, inda suka kashe mutane, suka yi garkuwa da wasu, da sace dabbobi, kafin a fatattake wasu.
Mazauna kauyuka 30 a Kaura-Namoda sun gudanar da zanga-zanga a Gusau, suna rokon gwamnati ta kawo karshen ta’addancin da ke halaka rayukansu kullum.
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kai hare-hare kan jama'a a kauyuka daban-daban cikin kwanaki huɗu, ana fargabar sun sace 150.
Rahotanni daga garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun nuna cewa ƴan bindiga sun sace mata matasa da suka fito samo itacen girki.
Rundunar ‘yan sandan Katsina da hadin gwiwar sojoji da KSCWC sun dakile hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan Faskari, an fatattaki miyagun su ba tare da asara rai ba.
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta dakile hare-hare biyu da aka kai a Sabuwa, inda ta ceto mutum 28. Amma 'yan ta'adda sun kashe mutane uku a harin.
'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago bayan sace su a jihar Zamfara. An sace mutanen ne a karamar hukumar Kaura Namoda.
Gwamnatin jihar Kwara ta sanar da kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane a jihohin Kwara da Kogi. Yan sanda sun ce jami'insu daya ya jikkata.
A Alkaleri, mahaifar gwamnan Bauchi, 'yan bindiga sun kashe mutum ɗaya yayin da suka yi garkuwa da mutane 26. An fara tura masu Naira miliyan 1.5 na kudin fansa.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari