Masu Garkuwa Da Mutane
Mahara sun kashe Oba Kehinde Jacob Falodun na Agamo a Ondo. Yan sanda da Amotekun sun fara bincike bayan an tsinci gawar sarkin da raunukan bindiga.
'Yan ta'adda sun saki bidiyon mazauna garin Woro 176 da suka sace a Kwara. A cikin bidiyon, an ga halin da mata da kananan yara suke ciki, yayin da suke neman dauki.
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane takwas da aka sace a wajen biki a jihar Kano. 'Yan bindiga sun saka kayan sojoji sun sace mutanen a karamar hukumar Shanono.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta cafke matasa uku da ake zargi da garkuwa da Alhaji Ahmadu, tare da gano ɗan mutumin da aka sace a cikin su.
'Yan bindiga sun sace masu ibada 9 a cocin Katolika dake Jihar Benue. Shugaban karamar hukumar Ado LGA da ƴan sanda sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun bi sawu.
Rahotanni daga yankin karamar hukumar Kauru sun nuna cewawaus mahara sun sheke mutane 3, sun sace Rabaran Nathaniel Asuwaye tare da wasu mutane 10.
Awanni bayan sun kubuta, wasu daga cikin kiristocin da aka sace a garin Kurmin Wali a Kaduna sun ce dun sha azaba matuka a hannun masu garkuwa da mutane.
Rahotanni daga Kurmin Wali sun tabbatar da cewa mutanen da yan bindiga suka yi garkuwa da su daga coci uku sun shaki iskar yanci a daren jiya Laraba.
'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu da ɗan uwanta a Pindiga, Gombe; ƴan sanda sun kashe mahara 3 tare da ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari