Manyan Labarai A Yau
Ladanin masallacin Harami da ke birnin Makka, Sheikh Ibrahim Al-Madani, ya rasu yana da kimanin shekaru 48, bayan shekaru yana kiran sallah a Harami.
Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamna, Alhaji Ibrahim Idris a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, Kingsley Fanwo, ya fitar
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi,Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu yana da shekaru 77 a birnin Landan na Birtaniya, bayan ya shafe shekaru tara yana mulkin jihar.
Kungiyar SERAP ta kai hukumar zabe ta INEC kotu kan zargin rashin bayyana iyakar kudaden da ‘yan siyasa da jam’iyyu za su iya karba gabanin zaben 2027.
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 2026.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce a shirye yake ya sasanta da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, yana mai cewa ya yafe masa kuma ba ya rike da gaba.
Mai girma Bola Tinubu, Atiku da Peter Obi na ƙoƙarin faɗaɗa sansanonin siyasarsu kafin zaɓen 2027, yayin da jam’iyyunsu ke neman ƙarin jihohi da goyon baya.
Tsohon Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai, Farouq Aliyu, ya ce ya ƙi N250m da aka ba shi domin ya goyi bayan ƙoƙarin Obasanjo na wa’adin mulki na uku.
Ƙungiyar Houthi da ke Yemen ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan wasu wurare masu muhimmanci a kasar Saudiyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari