Malaman Makaranta
Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu da ta biya su albashin watanni hudu da ta rike ko ta fuskanci fushin kungiyoyin.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda ta ke kashe N4b domin ciyar da dalibai 25,000 a makarantun kwana a jihar. Dakta Fauziyya Ada ce ta bayyana haka.
Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da shirin dawo da kai dalibai kasar Singapore domin cigaba da karatu. Gwamnan jihar, Umar A. Namadi ne ya sanar da haka.
Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar ta-baci a kan sha’anin ilmi. An fara ne da kara kason ilmi a kasafin kudin 2024. Abba zai kara daukar ma’aikata 10, 000.
Duk da Hadiza Shehu Galadanci ta zama Farfesa, ba ta manta da kula da iyalinta ba. Farfesar ta ce idan ta dawo daga asibiti, abin da yake gabanta shi ne tarbiyya.
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Oluhas ya ba da kyautar N10m ga dalibin da ya yi fice a jami’ar LASU, Olaniyi Olawale, wanda ya kammala da digiri da CGPA na 4.98.
Makarantar Ace da ke Garki, Abuja ta dakatar da wata daliba da mahaifinta ya shiga har cin makarantar ya lakaɗawa wata malama duka saboda ta ladabtar da ɗiyarsa.
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar daliban da ta rike. Dalibai 24,535 za su sake zana jarabawar UTME
Yayin da kungiyar kwadago ta shiga yajin aikin gama gari a wannan Litinin din, mambobinta sun tilastawa makaranta da bakuna bin umarnin yajin aiki a Kaduna.
Malaman Makaranta
Samu kari