Matawalle
Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta shiga maganar rigimar Dauda Lawal da Bello Muhammad Matawalle da kuma rigimar Aliko Dangote da Abdussamad Isiyaku Rabiu.
Tsohon gwamnan Zamfara kuma karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya zargi Gwamna Lawal da kulla masa makirci don a kwace kujerarsa. Ya karyata zargin rashawa.
Gwamnatin Zamfara zargi gwamnatin APC da ta wuce da taimakawa ‘yan bindiga da hawa kan dukiyar al’umma maimakon a samar da ruwan sha, tituna da sauransu.
Wasu masu zanga-zanga sun yi tattaki har zuwa zauren majalisar tarayya da ke Abuja ranar Laraba, sun buƙaci a tsige Bello Matawalle daga matsayin ministan tsaro.
Dauda Lawal Dare ya ce gwamnatin da ta shude ta Bello Matawalle ta saci kudi ta hanyar biya kusan duka kudin kwangilar a lokacin da ba a kai ga fara ayyukan ba.
Dauda Lawal ya fito da bayanai da za su gaskata zargin da yake yi wa Bello Matawalle. An tona yadda Matawalle ya yi bindiga da dukiyar Zamfara a aikin filin jirgi.
Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya karyata jita-jitar cewa su na tattaunawa da 'yan bindiga a asirce a Zamfara kamar yadda Gwamna Dauda Lawal ya yi zargi.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya bayyana cewa hukuncin da aka ji Kotu ta yanke ranar Litinin ɗin nan ya ƙara tabbatar da inda Zamfara suka karkata.
Kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a jihar Zamfara ta tabbatar da Gwamna Dauda Lawal Dare a matsayin zababben gwamna inda ta yi watsi da korafin Bello Matawalle.
Matawalle
Samu kari