
Lafiya Uwar Jiki







Bayan shafe watanni uku babu labarinsa, al'umma a jihar Taraba sun bukaci sanin halin da mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali ke ciki game da lafiyarsa.

Dakta Sam Adegboye ya musanta cewa yawan jima’i na rage hadarin sankarar maraina, yana mai bada shawarar gwajin PSA don tabbatar da lafiyar maraina.

Masarautar Zazzau ta yi rashin jigo a cikinta, Sarkin Yakin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate wanda ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Alhamis.

Kungiyar ma'aikatan jinya da unguwar zoma (NANNM) ta yi barazanar shiga yajin aiki a jihar Katsina. Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar ta samar da tsaro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu 'bleaching' sun yi yawa a Najeriya inda Ministan Lafiya ya nuna damuwa kan yadda ake kara amfani da kayan gyaran fata a Najeriya.

NAFDAC ta rufe kantin magani a Abuja kan sayar da kayan magani marasa rijista. Kayayyakin sun kai na N7m, kuma an cafke mutane biyu domin bincike.

Gwamnatin Kogi za ta kashe N7bn don gyara cibiyoyin lafiya 88, tare da goyon bayan Babban Bankin Duniya, don inganta kiwon lafiya a jihar cikin watanni huɗu.

Likitocin ARD-FCTA ta gargadi Wike kan yajin aiki mafi muni idan ba a biya bukatunsu ba cikin kwanaki 14, ciki har da albashi, kudin kayan aiki, da gyaran dokoki.

Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta fito da shirin tallafawa 'yan Najeriya wajen saya musu magani domin rage radadin matsin rayuwa saboda matsin tallali
Lafiya Uwar Jiki
Samu kari