Labarin Sojojin Najeriya
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar cafke wani dan ta'addan ISIS a Borno. Ana ci gaba da gudanar da bincike.
Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP a Borno tare da ƙwato kyamara mai ɗauke da bayanai kan ƙwararrun ƴan ta'adda daga ƙasashen waje.
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun bayyana yadda suka rika daukar matakai domin ceto daliban da aka sace a wata makaranta a jihar Oyo bayan garkuwa da su.
A labarin nan, za a ji yadda wata marya ta rasa rayuwarta tana cikin gida a lokacin da Boko Haram da sojojin kasar nan suke gwabzawa a jihar Borno.
Matashi ma fafutuka a kafafen sada zumunta Justice Crack ya musanta zargin Ministan Tsaro Christopher Musa cewa ya umarci sojoji su cire nama daga abincinsu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi zama na musamman da hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban kasa tare da jami'an leken asiri, Ribadu da sauransu.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasarar cafke wata 'yar kasar Chadi mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda.
An samu barkewar cutar amai da gudawa a wani sansanin 'yan ta'addan ISWAP da ke jihar Borno. Barkewar cutar ta jawo mayaka da dama sun sheka zuwa barzahu.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa gwammatin tarayya ta sake duba albashin sojoji domin inganta walwalarsu a Najeriya.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari