
Labarin Sojojin Najeriya







'Yan bindiga na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kisan manyan jahororinsu da jami'an tsaro suka yi a Zamfara. Sun yi awon gaba da mutane masu yawa.

Mashawarcin shugaban kasa, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa dole ne a samu hadin kan jama'a idan har za a yaki matsalar rashin tsaro da gaske a jihar Filato.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta fusata bayan cin karo da labaran dake cewa an biya 'yan ta'adda kudin fansa kafin su saki tsohon shugaban hukumar NYSC.

An shiga jimami a jihar Kebbi bayan 'yan ta'addan Lakurawa sun kai farmaki kan 'yan sa-kai. Miyagun 'yan ta'addan sun hallaka jami'an tsaro 13 a yayin harin.

Dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu mai tsanani da 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. An samu asarar rayuka a bangarorin sojoji da na 'yan Boko Haram.

Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasara kan miyagun 'yan bindiga a jihar Taraba. Sojojin sun hallaka miyagu tare da kwato makamai.

An bukaci kafa sansanin soji a garin Uromi na jihar Edo bayan kashe Hausawa matafiya ana shirin bikin sallah. sarkin Uromi, Zaiki Anslem Eidenojie II ya nemi hakan.

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin raba Bello Turji da numfashi nan da ba daɗewa ba bayan kisan manoma 11 da ya yi a yankin ƙaramar hukumar Isa a Sokoto.

Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta fitar da bayanai kan kisan gillar da ka yi wa mafarauta 'yan Arewa a jihar Edo. Ta bayyana cewa an shawo kan matsalar.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari