Labarin Sojojin Najeriya
Laftanar Adam Muhammad Yerima ya yi aure a asirce da masoyiyarsa da ake kira Khadija a jihar Kaduna, bayan makonni da ce-ce-ku-ce kan rayuwarsa ta sirri.
A labarin nan, za a ji cewa wasu miyagun matasan ƴan ta'adda sun kashe Zamfarawa a ƙauyensu saboda an hana su satar madarar roba a wani shafi, sun yi fashi.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi magana kan maganar ministan tsaro cewa ba za a yi sulhu da 'yan bindiga ba a Najeriya.
Sabon Ministan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya sha alwashi kan tsaron Najeriya. Janar Christopher ya kuma yi godiya kan son da aka nuna masa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro. Hakan na zuwa ne bayan majalisa ta amince da shi.
Sabon ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana cewa ba za a cigaba da sulhu da 'yan ta'adda ko biyan kudin fansa ba.
Wasu jami'an 'yan sanda da sojoji sun ba hamata iska a jihar Filato. Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa ta dauki mataki tare da hukunta masu laifi.
Sabon ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa zai yi matukar kokarin wajen hana kashe kashe a Najeriya bayan zama ministan tsaro.
Wani lauya mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya yaba da nadin tsohon babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaron Najeriya.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari