Labaran Duniya
Sabuwar annobar cutar Ebola da ta bulla a DR Congo ta kashe mutane 15, WHO ta ce tana aiki cikin gaggawa tare da amfani da rigakafin Ervebo domin dakile cutar.
Shugaba Donald Trump ya karyata jita-jitar mutuwarsa da ta bazu a shafukan sada zumunta, ya ce bai taba jin wannan labarin ba sai da aka tambaye shi.
Duk da cewar Yammacin duniya irin su Amurka na da tasiri, saurin karuwar jama’a a Afirka da Asiya na kokarin sauya cibiyar tasirin Kiristanci zuwa Kudancin duniya.
Wani luguden wuta na bam daga sojojin Isra’ila ya kashe Firaministan Houthi mai ikirari, Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi, da wasu jami’an ƙungiyar Houthi a Sanaa.
An hallaka tsohon kakakin majalisar dokokin Ukraine, Andriy Parubiy, a Lviv, abin da ya tayar da hankula a kasar, yayin da shugabanni ke aika wa da sakon ta’aziyya.
Wani dan Najeriya Daniel Chima Inweregbu ya amsa laifin da gwamnatin Amurka ke tuhumarsa da aikatawa na damfarar soyayya ta intanet, za a hukunta shi.
Yayin da ake shirin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a watan Satumbar 2025, kasar Amurka ta hana shugabannin Falasɗinu shiga taron a New York.
Rahotanni daga kasar Mexico sun nuna cewabsanatoci su ba hammata iska a zaman ranar Laraba, inda lamarin ya kai ga doke doke da ture-ture a zauren Majalisa.
Kotun Equatorial Guinea ta yanke wa Ruslan Obiang Nsue, dan shugaban kasa, hukuncin shekara shida bayan samunsa da laifin sayar da jirgin gwamnatin kasar.
Labaran Duniya
Samu kari