
Labaran Duniya







Dandalin sada zumunta na X ya daina aiki a cikin kasar Brazil mai mutane miliyan 200, sakamakon kazamin fada tsakanin Elon Musk da wani alkali dan kasar.

Cikakken jerin jami’o’i 7 da suka karrama Aliko Dangote da digirin girmamawa a bisa irin gudunmawar da ya ke bayarwa wajen kasuwanci da ayyukan jin kai.

Wani rahoto ya nuna yadda 'yan bindigar Najeriya suka fara amfani da manhajar TikTok suna tallata ayyuk ansu. Mun tattaro kasashen da aka haramta manhajar.

Gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen jami'o'in kasashen Benin da Togo da ta amince daliban Najeriya su je su yi karatu domin neman digiri da nufin tsaftace ilimi.

Hukumomi a kasar Faransa sun cafke mai kamfanin Telegram, Pavel Durov. An tsare attajirin ne wanda ya taho daga kasar Azerbaijan bayan ya sauka a filin jirgi.

Kamfanoni hudu daga kasashen Togo da Benin sun gaza biyan Najeriya dala miliyan 14.19 na kudin wutar lantarkin da aka tura masu a watanni 3 na farkon 2024.

Daliban da suka kifar da gwamnatin kasar Bangladesh a yayin zanga zanga sun bayyana halin da suke ciki a asibiti. Ma'aikatan lafiya ta bayyana yadda suke aiki.

An kama Yomi Jones Olayeye, dan shekara 40 dan Najeriya daga Legas, a filin jirgin sama na John F. Kennedy da ke birnin New York bisa zargin zamba na COVID-19.

Rahotanni sun bayyana cewa Maria Branyas, wadda ta fi kowa a duniya ta mutu tana da shekaru 117. An ruwaito cewa an haifi Maria a 1907 kuma ta mutu a Spain.
Labaran Duniya
Samu kari