Zaben jihohi
Akalla ciyamomin kananan hukumomi 21 suka bar ofisoshinsu da kuma kansiloli 239 a jihar yayin da su ka kammala wa'adinsu na shekaru uku a kan kujerun.
Gwamnonin jihohi 19 na Arewa sun shiga wata ganawa a jihar Kaduna don tattauna batun tsaro da tattalin arzikin shiyyar. Sai dai akwai gwamnoni 6 da ba su halarta ba.
Gwamnatin jihar Kebbi ta sha alwashin korar duk wani kwamishina da ya siyar da motar da gwamnatin ta ba shi. Akalla kwamishinoni 26 ne suka samu kyautar mota.
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya sanar da daukar hutu a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023 don zuwa neman lafiyarsa. Aiyedatiwa zai zama gwamna.
Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan shari'ar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP a Kogi, Murtala Ajaka da Gwamna Yahaya Bello inda ta ce tararsa miliyan 500.
Kakakin majalisar jihar Nasarawa, Jatau, ya sanar da nade-naden da suka hada da na shugaban masu rinjaye da mataimakinsa, sai kuma bulalar majalisar.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Edo, Asue Ighodalo ya gagara isar da sako ga kabilarshi inda ya nemo mai fassara don isar da sako a gare su..
Gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi da birnin Abuja N135bn a karkashin tsarin NG-CARES. Nasarawa da Kuros Ribas sun fi kowane samun kaso mai tsoka.
Dan takarar jam'iyyar NNPP, Farfesa Sani Yahaya ya garzaya Kotun Koli don kalubalantar shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba da ta tabbatar da nasarar PDP.
Zaben jihohi
Samu kari