Zaben jihohi
Dan takarar gwamnan Edo karkashin jam'iyyar AAC, Udoh Oberaifo ya ce ya tsallake hare-hare 'yan bindiga da ke son kashe shi har sau uku a wajen yakin neman zabe.
Kotun kolin Najeriya ta kori ƙarar da tsohon ƙaramin ministan man fetur ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaben Bayelsa, ta tabbatar da nasarar Douye Diri.
Jam'iyya mai mulki a Kano, NNPC ta sayawa kwamitin tantance yan takarar katin duba jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma yi masu gwajin kwaya.
Shugaban hukumar zabe INEC reshen jihar Ogun, Barista Niyi Ijalaye ya yanke jiki ya faɗi kuma Allah ya masa rasuwa bayan fitowa daga taro a Abuja.
An rantsar da wani matashi, Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo, mai shekaru 28 a matsayin shugaban karamar hukumar Toro a jihar Bauchi. An ce matashi ne mai hazaka.
Kimanin magoya bayan jam'iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya a jihar Ondo ne suka sauya sheka zuwa PDP. Dakta Adeniran Oyebade ne ya jagoranci tawagar.
Kotun kolin ta ajiye hukunci kan karar da jam’iyyar adawa ta APC da dan takararta Timipre Sylva suka shigar na kalubalantar nasarar gwamnan Bayelsa Douye Diri.
Kotun Koli da ke zamanta a birnin Tarayya Abuja ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo da Murtala Ajaka na jam'iyyar SDP.
A yau Litinin 19 ga watan Agustan 2024 Kotun Koli ta fara zaman karshe kan shari'ar takaddamar zaben gwamnan jihar Kogi da Bayelsa da aka gudanar.
Zaben jihohi
Samu kari