Zaben jihohi
Rundunar sojojin Najeriya sun tura jami’ansu zuwa jihar Ondo domin tabbatar da tsaro a zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2024.
A yayin da ake shirin zaben Ondo, mun tattaro muku jihohin Najeriya da ke karkashin APC da PDP. Gwamnonin da za su gama da masu tazarce a nan gaba.
Akwai manyan 'yan takara 4 a zaben gwamnan Ondo na 2024,: Lucky Aiyedatiwa (APC), Ajayi Agboola (PDP), Otunba Bamidele Akingboye (SDP), da Sola Ebiseni (LP).
A ranar Asabar, mazauna jihar Ondo za su sake zabar gwamna wanda zai yi wa’adin shekara hudu a kan mulki, kuma akwai laifuffuka da ya dace yan siyasa su lura da su.
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya fadi gwagwarmayar takara da yayi a zaben 1999. Obasanjo ya yi fatan alheri ga dan takarar APC a zaɓen Ondo.
Jam’iyyar APC ta lashe dukkan kujerun shugabanni 13 da mafi rinjayen kujerun kansiloli a zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa da aka kammala ranar Asabar.
Hukumar zaben jihar Abia, ABSIEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi inda ZLP da YPP suka lashe kujerun yayin da LP mai mulki ta barar.
Shugaban malaman addinin Musulunci a jihar Ondo ya goyi bayan dan takarar gwamnan APC a zaɓen Ondo. Malaman Musulunci sun ce za su zabi APC a Ondo.
Babban sarki a jihar Ondo, Oba Olufaderin Adetimehin ya goyi bayan dan takarar gwamnan APC a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi a shekarar 2024 da muke ciki.
Zaben jihohi
Samu kari