Zaben jihohi
Gwamna Farfesa Charles Chukwuma Soludo na Anambra na daga cikin yan takara da aka fafata da su a neman wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar APGA.
Dan takarar jam'iyyar Labour Party a zaben gwamnan jihar Anambra, Dr. George Moghalu, ya bayyana cewa rashin sayen kuri'u ne ya sanya ya fadi a rumfar zabensa.
A labarin nan, za a ji cewa yar takarar gwamnan Anambra ta bayyana godiya ga mutane kusan 300 da su ka kada mata kuri'a a zaben da Charles Soludo ya yi nasara.
Dr. Wole Oluyede ya lashe zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na PDP a jihar Ekiti don zaɓen 2026. PDP ta sha alkawarin kayar da APC saboda gazawar gwamnatin Oyebanji.
Wasu ‘yan bindiga sun harbe kansilan jam’iyyar APGA, Nze Ala Kuru Orji, yayin da yake jefa ƙuri’a a mazabar Ezukaka 1, Orumba ta Kudu a jihar Anambra.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya aika sako bayan sake lashe zabe. Ya yabawa mutanen jihar kan sake ba shi kuri'un da suka yi.
Hukumar zabe ta INEC ta ayyana Gwamna Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Anambra da aka gudanar ranar Asabar.
Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe dukkan kananan hukumomi 21 a zaben gwamnan Anambra, inda ya samu kuri’u 422,664, sannan APC ta samu 99,445.
Bayan dawo wa daga dan takaitaccen hutu, hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Anambra ta Yamma, inda nan ma Soludo na APGA ya lashe zabe.
Zaben jihohi
Samu kari