Labaran garkuwa da mutane
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban wata makarantar firamare a jihar Oyo tare da neman Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa kafin sakinsa.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatat da cewa wasu jami'anta ke rakiyar gawar abokin aikinsu zuwa gida sun fada tarkon 'yan bindiga a jihar Kogi.
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun bayyana yadda suka rika daukar matakai domin ceto daliban da aka sace a wata makaranta a jihar Oyo bayan garkuwa da su.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tuna baya kan yadda 'yan bindiga suka sace wasu 'yan uwansa. Gwamna Dauda ya bayyana cewa ya ki ba su ko sisin kwabo.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da ceto wadanda yan bindiga suka yi garkuwa da su a coci a jihar Ekiti, sun ce mutum daya ya rasa ransa a hannun masu garkuwa.
A labarin nan za a ji cewa rundunar yan sandan jihar Anambra ta kama wani mutum da ya zambaci abokinsa ta hanyar sace masa yaro, ya sayar a kan N1.3m.
Rahotanni sun nuna cewa barci ya dauke wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane bayan sace wasu jama'a, inda jama'ar suka tsere suka gudu daga dajin.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta tura dakaru zuwa yankin bayan samun labarin kashe almajirai da garkuwa da wasu yan gida daya a jihar Bauchi.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa a kan batun Malama UmmulKhairi ba.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari