
Shafukan ra'ayi da sada zumunta







Kungiyar SERAP ta shigar gwamnatin Bola Tinubu da gwamnoni 36 a kotu kan amfani da dokar laifuffukan yanar gizo (Cybercrimes) don tauye 'yancin fadin albarkacin baki

Gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sadarwa su yi ƙarin kudin kiran waya, sako da sayen data amma ba zai kai kaso 100% ba in ji ministan sadarwa, Bosun Tijani.

Ministan sadarwa na Najeriya, Bosun Tijani ya shiga taro da wakilan kamfanonin sadarwa da ke aiki a kasar nan kan bukatarsu na kara kudin kira da data.

Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun yi koken cewa hauhawar farashi a kasar ya shafe su, saboda haka ne suke bukatar a sahale masu karin farashin waya.

Wani saurayi ya siya wa fitacciyar 'yar TikTok a Arewa, Maryam Sa'idu gida na N55m, ya ce ta daina zama a otel. Maryam ta ce ba za ta yi aure ba sai Tinubu ya sauka.

An gurfanar da Mahadi Shehu a gaban kotun majistare a Kaduna bisa zargin hada baki, tallafa wa ta'addanci, da tayar da rikici inda aka tura shi gidan kaso.

Rundunar 'yan sandan Kano ta babban kuskure ne tare hanyoyin da jama'a ke bi. An gargadi 'yan soshiyal madiya masu rufe hanyoyi su na daukar bidiyo sabodaabiyansu.

Masu amfani da shafukan Facebook, Instagram da WhatsApp sun fuskanci matsala. Tangarɗar ta shafi sassa da yawa a faɗin duniya, inda kamfanin META ya fara gyara.

An zargi wasu ƴan ƙasar nan da ƙin ci gaban Naira. Wannan na zuwa bayan an sayar da Dala a kan N1,555 a ranar Juma'a. Reno Omokri ya soki ƴan ƙasar nan.
Shafukan ra'ayi da sada zumunta
Samu kari