Kasashen Duniya
A cewar asibitin a shafin Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, kuma tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar. Dattijuwar ta kafa tarihi a Afrika.
Sanatocin Arewa sun yi wani zama. su ka bukaci Bola Tinubu ya maidawa Nijar wutan da aka yanke, a bude filin jirgin sama, sannan Sojojin Nijar su bar mulki a 2025.
Fadar Shugaban kasa ta bada sanarwa a yau cewa Bola Tinubu zai kasar waje. Bola Tinubu zai tafi Dubai a kasar UAE ne domin halartar taron COP28 da za ayi.
Dokin zuciya ya ja wani ango ya kashe amaryarsa, kanwarta da surukarsa a ranar aurensu a lardin Arewa maso Yammacin kasar Thailand. Ya kuma harbi wasu hudu.
Kungiyar SERAP ta bukaci Bankin Duniya da ya dakatar da ba jihohin Najeriya rancen kudi kan zargin almubazzaranci. Ana bin jihohin bashin naira tiriliyan 9.17.
An samu fargabar yin juyin mulki a kasar Saliyo lokacin da wasu yan bindiga suka kai farmaki a wani barikin sojoji tare da kokarin kwace wajen ajiyar makamai.
Gwamnatin Birtaniya na gayyatar dalibai daga Najeriya da wasu kasashe 14 don neman tallafin karatu daga gidauniyar GREAT gabanin zangon karatu na shekarar 2024-25.
Wannan damar ta hada da tallafin sufuri, alawus-alawus na wata-wata, shawarwari kan gidajen zama, kula da lafiya, kudaden biza, da kuma kudaden karatun kasar.
Matasan sun gamu da ajalinsu ne a wajen tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama
Kasashen Duniya
Samu kari