Karatun Ilimi
A karon farko a tarihin Kano, Abba Kabir Yusuf ya warewa sha'anin ilmi kusan 30%. Hassan Sani Tukur ya ce banagaren ilmi zai tashi da kaso mai tsoka a kasafin kudi.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu ma’aiakatan gwamnati guda biyu kan zargin sayar da takardun aiki ga mazauna jihar.
Gwamnatin Kano ta zargi tsohuwar gwamnatin da gazawa wajen inganta ilimi bayan ta samu dalibai miliyan 4.7 na zama a kasa babu kujeru a makarantunsu.
Hukumar da ke lura da asusun bayar da lamunin karatu na kasa (NELFUND) ta tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa za ta bawa daliban da su ka dace lamunin karatun.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya mazauna jihar murnar zagayowar ranar dimukuradiyya a Najeriya tare da bayanan halin da gwamnatinsa ta ke ciki.
Wani kansila a jihar Kano ya dauki nauyin karatun marayu 120 tun daga karama har zuwa babbar sakandire. Ya kuma yi alkawarin tallafa masu ko ba ya kan mulki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gina dakunan bincike 300 da samar da malamai 10,000 domin inganta ilimi a jihar. Hakan ya biyo bayan dokar ta baci ga ya saka ne.
Duk da Hadiza Shehu Galadanci ta zama Farfesa, ba ta manta da kula da iyalinta ba. Farfesar ta ce idan ta dawo daga asibiti, abin da yake gabanta shi ne tarbiyya.
Gwamnatin Gombe ta dauki matakin kawo tsarin zamani cikin harkar almajiranci a jihar. Mai ba gwamnan shawara kan almajiranci, Aminatu Dahiru Bauchi ce ta fadi haka
Karatun Ilimi
Samu kari