Jirgin Sama
Jiragen yakin Amurka biyu sun yi karo a sama yayin wasan kwaikwayon jirage a Idaho, amma matuka guda hudu sun tsira kafin jiragen su tarwatse da suka fado kasa.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya nuna tsantsar farin ciki yayin jirgi na farko dauke da maniyyata ya tashi daga filin jirgin Gusau zuwa kasa mai tsarki.
Jirgin kamfanin Max Air da ya tashi daga Abuja zuwa Katsina ya yi gaggawar sauka bayan samun matsala a inji, fasinjoji sun ce hankalinsu ya tashi.
Kamfanin sufurin jiragen sama na Rano Air ya dakatar da harkokinsa a wasu hanyoyi a Najeriya saboda tsadar farashin man jirgi, ya ce matakin na dan lokaci ne.
An fitar da rahoto bayan bincike da aka yi game da wani jirgin China da ya yi hadari a shekarar 2022. An bayyana cewa an katse man fetur din da aka sawa jirgin.
Mutum 14 sun rasu a hatsarin jirgin sama a Sudan ta Kudu sakamakon rashin kyawun yanayi, yayin da wasu suka kwashe miliyoyin daloli a hatsarin jirgi a Paraguay.
Kamfanonin masu zirga-zirga da jiragen sama sun fara barazanar tafiya yajin aiki a Najeriya saboda tsadar man da suke amfani da shi a fadin kasar nan.
Kungiyar Hezbollah da ke marawa Iran baya ta kai farmaki kan jirgin Isra'ila yayin da ya yi yunkurin kai farmaki a kasar Lebanon. Isra'ila bata ce komai ba.
Gwamnatin kasar Colombia ta tabbatar da hadarin jirgin sojojin samanta dauke da mutane sama da 100. An bayyana cewa mutum 64 ne suka rasu a hadarin.
Jirgin Sama
Samu kari