Jihar Kogi
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yi nade nade a gwamnatinsa. Gwamnan na jam'iyyar APC ya nada sababbin manyan sakatarori guda 12 a jihar.
Gwamnatin jihar Kogi ta wanke Gwamna Usman Ododo bayan da ce-ce-ku-ce ya barke yayin da aka ganshi tare da wasu gwamnonin PDP a Jalingo, babban birnin Taraba.
Yayin da ake zargin Gwamna Ododo da shirin sauya sheka zuwa PDP, gwamnatin jihar Kogi ta fayyace gaskiya inda ta ce kwata-kwata babu wannan shiri.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya nuna farin cikinsa kan nasarar da ya samu a Kotun Koli kan shari'ar zaben gwamnan jihar. Ya ba 'yan adawa shawara.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kogi ta yi iƙirarin cewa an farmaki magoya bayanta a harabar kotun koli bayan tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Ododo ranar Jumu'a.
Wasu yan daba da ake zargin yan APC ne sun farmaki dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka bayan hukuncin Kotun Koli a birnin Tarayya Abuja.
Bayan yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Bayelsa, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Kogi.
Hukumar da ke yaki da rashawa ta EFCC, ta ce tana aiki da jami'an tsaro na cikin gida da na waje domin kama da Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi
Kotun daukaka kara ta umurci tsohon gwamna, Yahaya Bello da ya mika kansa domin a gurfanar da shi a gaban kuliya. Kotun ta yi watsi da hukuncin wata kotun Kogi.
Jihar Kogi
Samu kari