Jihar Kano
Ana fargabar gobara ta jawo asara mai tarin yawa a fadar Sarkin Kano bayan iftila'in da ya faru a daren jiya Juma'a 12 ga watan Yuli 2024 a fadar da ke Kofar Kudu.
Jigon jam'iyyar APC a Kano, Dan Bilki Kwamanda ya yi martani kan kura-kuran da gwamnatin Bola Tinubu ke aikatawa a Najeriya inda ya ce zai samu matsala a zabe.
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan korarsa da aka yi a jam'iyyar NNPP inda ya ce babu wanda ya isa bayan su ne gatan jami'yyar.
Yayin da ake tsakiyar taƙaddama kan sarautar Kano, Sanata Masud Doguwa ya sanar da cewa shi da magoya bayansa sun hakura da tafiyar APC, sun koma PDP a Kano.
Dalibai da malaman jami'ar Bayero sun shiga alhini bayan rasuwar Farfesa mai matsalar gani na farko a Najeriya, Farfesa Jibril Isa Diso.Kafin rasuwarsa malami a BUK.
Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano ya gabatar da kudurin samar da asibitin kwararru a karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano ga majalisa. an yi karatu na daya.
Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Ajingi/Albashi/Gaya, Hon. Ghali Mustapha ya caccaki mataimakin kakakin Majalisar, Benjamin Kalu kan nuna wariya.
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya caccaki matasa kan zanga-zanga inda ya ce ba su da tarbiyya ganin yadda suke cin mutuncin malamai.
Yayin da ake fafutukar ganin jama'a a Kano sun dauki aure da daraja, sai ga wani magidanci ya saki matarsa a gadon asibiti saboda an hana shi sadakar da aka ba ta.
Jihar Kano
Samu kari