Jihar Kano
Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta kwace ragamar shugabancin NNPP a hannun tsagin Rabiu Kwankwaso. Ta ce ba za ta shiga rikicin jam'iyya ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an mayar da Sarkin Gaya kan kujerarsa saboda jajircewarsa da tawali'u a lokacin da aka tube shi a shekarar 2023.
An aci gaba da jimami kan kisan gillar da aka yi wa mafarauta 'yan Arewa a jihar Edo. Bayan aukuwar lamarin, wasu muhimman abubuwa da dama sun faru.
Bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi a ranar Talata 1 ga watan Afrilun 2025, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na ci gaba da karbar ta'aziyya.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ), ta fitar da bayanai kan kisan gillar da ka yi wa mafarauta 'yan Arewa a jihar Edo. Ta bayyana cewa an shawo kan matsalar.
Al'ummar Kano da ke zaune a Kofar Nasarawa sun shiga tashin hankali da gobara ta tashi a 'Gidan Ado Bayero' wanda yake matsayin matsugunnin jami'ar Arewa maso Yamma.
Bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya soke duk wasu shirye-shiryen bukukuwan sallah da aka tsara.
Rundunar ƴan sandan Kano ta fara gudanar da bincike kan zargin karaya dokar da ta kafa ta hana hawan Sallah, ta gayyaci Shamakin Kano don ya amsa tambayoyi.
Jama'a da dama a Kano sun bayyana fatan yadda rasuwar Galadiman Kano ya zaunar da Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Abbas a inuwa guda, za a ci gaba da hadin kai.
Jihar Kano
Samu kari