
Malamin addinin Musulunci







Kungiyar Izala ta yi sababbin nade nade. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya nada Malam Dalhatu Abubakar Hakimi a gurbin marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir.

Malamin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya yi wa'azi a masallacin Dr Idris Dutsen Tanshi a Bauchi. Bello Yabo ya fadi alakarsa da Dutsen Tanshi tsawon shekaru 30.

Malamin Musulunci a Najeriya, Imam Junaidu Abubakar Bauchi ya ƙaryata labarin cewa ya rasu inda ya ce yana cikin koshin lafiya ba kamar yadda ake yadawa ba.

Babban malamin Izala, Imam Bello Jandutsi ya rasu a Birnin Kebbi bayan shekaru 30 yana limanci da da’awa. Za a yi jana’izarsa a masallacin Sheikh Abbas, Rafin Atiku.

Yayin da ake ci gaba da ta'aziyyar Malam Idris Dutsen Tanshi, dalibai da iyalan marigayin sun sake fitar da wata sanarwa, suna jan hankalin al'umma kan ɗaukar hoto.

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dr Idris Dutsen Tanshi. Gwamnan ya mika filin Idin Games Village ga daliban Dutsen Tanshi.

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Harun ya rasu a jihar Gombe. Malamin ne limamin barikin 'yan sanda a jihar kuma shugaban daliban jami'ar Madina.

Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya yi kra ga Sheikh Sani Yahaya Jingir da Sheikh Abdullahi Bala Lau da su sake haduwa waje daya. Dr Jalo Jalingo ya goyi bayan kiran.

An gano wani tsohon bidiyo da marigayi ke zuba ruwan addu'o'i ga Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi kan yaki da Boko Haram da ya yi lokacin yana raye.
Malamin addinin Musulunci
Samu kari