Addinin Musulunci da Kiristanci
EFCC ta ce akwai kungiyoyi da shugabannin addini dumu-dumu a harkar satar kudin jama’a. A lokacin da ake da malamai na Allah, akwai wadanda abin duniya ne gabansu.
Jama’a sun yi ca a kan Gwamnan Filato saboda nunawa musulmai wariya. Bayanai sun fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar Filato, Arc. Samuel N. Jatau.
Gwamnatin jihar Oyo ta rufe wani babban coci a birnin Ibadan da ke jihar saboda yawan damun jama'ar yankin da kararraki wanda ya hana su sakat a gidajensu.
Kotu ta ci tarar wani kamfanin Amurka, Blackwell Security Services Inc., dala dubu 70 saboda ya tilasta wani sabon ma'aikaci Musulmi ya aske gemunsa.
Fasto Olabisi Adegboye ya fallasa wadanda ke juya gwamnatin Tinubu da kuma hana shi yin abin kirki a kasar inda ya ce za a kore su kafin cika shekara daya.
Rahotanni sun nuna cewa gobara ta tashi a cocin Household of David da ke karamar hukumar Ikeja a jihar Legas. Hukumar kashe gobara ta jihar Ta tabbatar da lamarin.
Rundunar tsaro a Najeriya ta yi martani kan zargin hannu a kisan Plateau inda ta shawarci mutane su yi watsi da jita-jitar kan cewa su na goyon bayan bangare daya.
Al'ummar da ke zaune a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato sun zargi jami'an tsaron jihar na 'Operation Rainbow' da aikata laifukan kisan kai da kona gidaje.
Za a ji yadda mace ta haihu a tsakiyar jama’a yayin da aka hallaka mazaje a kashe-kashen Filato. Akwai wanda take shirin aurar da yaronta da ta rasa komai a duniya.
Addinin Musulunci da Kiristanci
Samu kari