INEC
A yayin da al’ummar Edo ke shirin kada kuri’a a zaben sabon gwamna a ranar Asabar, 21 ga Satumba, mun yi cikakken bayani kan laifuffukan zabe a Najeriya.
A labarin nan, za ku ji cewa a ranar Asabar mai zuwa ne mazauna jihar Edo za su nufi rumfunan zabe domin sake zabar gwamna bayan Godwin Obaseki ya cinye wa'adinsa.
Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta fara jigilar kayayyakin zaben gwamnan jihar Edo daga Abuja. Rundunar ta ce hakan zai ba INEC damar yin shiri da wuri.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum, ya sha alwashin cewa za su kare kuri'unsu da jininsu a zaben gwamnan jihar Eɗo da ke tafe.
Yayin da ake ta korafi kan sanar da nasarar Bola Tinubu a zaben 2023, INEC ta fayyace dalilin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da tsakar dare.
Shugaban hukumar zabe INEC reshen jihar Ogun, Barista Niyi Ijalaye ya yanke jiki ya faɗi kuma Allah ya masa rasuwa bayan fitowa daga taro a Abuja.
Hajiya Hauwa Kulu Muhammadu Jega, mahaifiyar tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta rasu, za a yi jana'iza da karfe 1:30 na rana yau Asabar a Abuja.
Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta INEC ta musanta zargin akwai tuntuɓen alkalami a sakamakon zaben shugaban kasa da aka sanar da wanda aka shigar a IREV.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, ta sanya lokacin da za ta gudanar da zabe a kananan hukumomi 44 na jihar. Ta kafa sharudda ga 'yan takara.
INEC
Samu kari