Jihar Imo
Mutanen Abuja sun shiga zullumi lokacin da gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okoracha ya ruguje. Gidan mai hawa biyar. Anceto mutane uku daga baraguzan.
Shugaban majalisar dokokin jihar Imo, Chike Olemgbe ya sanar da dakatar da ƴan majalisa 4 bisa zarginsu da kulla yadda za su tunuke shi daga mukaminsa.
Rundunar sojin Najeriya ta kwato makamai a hannun yan ta'adda a jihohin Imo da Kwara. Rundunar ta yi nasarar cafke wasu manyan yan bindiga a jihohin yayin farmakin.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Imo, CP Ɗanjuma ya ce rundunarsa ba za ta bari ko ɗaya daga cikin ƴan bindigar da suka kai hari yankin Okigwe ya tsira ba.
Gwamnatin jihar Imo ta musanta zargin NLC ta ƙasa kan biyan mafi ƙarancin albashi, ta ce tuni ma'aikata suka fara jin alat na N40,000 mafi karanci a jihar.
Dakarun sojojin sama sun yi nasarar lalata haramtattun wuraren tace man fetur a jihohin Imo, Rivers da Bayelsa. Sun kuma lalata kayayyakin da ake amfani da su.
Wasu yan bindiga su hudu sun kai hari kan jami'an yan sanda a safiyar yau talata inda suka kashe yan sanda biyu da farar hula daya. Mutanen yankin suna zaman dar dar
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta dauki mataki kan wani faifan bidiyo na wani jami’in ‘yan sanda da aka nada yana karbar cin hanci daga hannun direbobi.
Kotun sauraran kararrakin zaben jihar Imo ta tabbatar da nasarar Gwamna Hope Uzodinma na jami'yyar APC a matsayin zaɓabben gwamnan jihar a yau Juma'a.
Jihar Imo
Samu kari