Jihar Gombe
Mutane 7 daga ƙauyen Lawanti a Gombe sun rasu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri yayin da suke kan hanyar zuwa biki, in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Wani matashi mai shekaru 19 a duniya da ke ƙungiyar mafarauta, ya rasu sakamakon fashewar bindiga bisa kuskure a unguwar Alkahira da ke Jihar Gombe.
Wani ma’aikacin wucin-gadi a Gidan Gwamnatin Jihar Gombe ya rasu a cikin yanayi mai cike da tambayoyi. 'Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da hannu a kisan.
Gwamnonin Arewa 19 sun yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai wani masallacin Juma'a a Maiduguri, jihar Borno, sun mika sakon ta'aziyya da jaje.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sallami hadimansa guda hudu nan take bisa dukan kansilan Shamaki da ya bayyana a bidiyo mai yawo.
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Gombe, ta harzuka bayan hadimin gwamna ya lakadawa Kansila dukan tsiya. Ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.
Babbar kotun jihar Gombe ta yanke wa basarake da wani mutum daya hukuncin kisa ta hanyar rataya, tare da wanke mutum 3 da aje tuhumarsu tare bisa laifin kisan kai.
An gano wani faifan bidiyo inda hadimin shugaban ma'aikatan gwamnatin Gombe ke zabgawa kansila masuka kan zargin ya ce zai mari mai gidansa saboda wai an biya shi.
Kungiyar Izalah (JIBWIS) reshen Gombe ta sanar da rasuwar shugabanta a Kwamin Yamma, Alhaji Abdullahi Barde wanda aka yi jana'izarsa a yau Talata.
Jihar Gombe
Samu kari