Jihar Gombe
An kama wani matashi mai shekaru 31 bisa zargin ya yiwa 'yar uwarsa kisan gilla a unguwar Bagadaza da ke jihar Gombe. Ya zuwa yanzu ana bincike kafin gurfanar dashi.
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) a jami'ar jihar Gombe ta janye yajin aikin da ta shiga. Ɗaliban jami'ar Gombe za su koma makaranta bayan yajin aiki.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na TCN ya bayyana cewa har yanzu bai gano abin da ya jawo daukewar lantarki a jihohin Arewa ba. Ana ƙoƙarin dawo magance matsalar.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa al'ummar jihar Jigawa kan iftila'i da ya afku inda suka ba da gudunmawar N900m.
An tattara jerin gwamnonin Najeriya da ke biyan mafi karancin albashi fiye da na gwamnatin tarayya. An yi mamaki yadda gwamnatin Gombe za ta biya fiye da N70,000.
Yayin da rikicin jam'iyyar PDP ke kara ƙamari, tsagin jam'iyyar PDP ta nada sabon mukaddashin shugabanta ta kasa a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.
Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da fara biyan mafi karancin albashin N70,000 yayin da ake cikin mummunan hali na tsadar rayuwa a fadin Najeriya baki daya.
Yayin da ake rigima kan halacci ko haramcin carbi a Musulunci, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi tsokaci kan lamarin inda ya ba Farfesa Ali Pantami shawara.
A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya kafa wata babbar tawagar tattaunawa da shugabannin ASUU da sauran kungiyoyin kwadago na jami'ar Gombe.
Jihar Gombe
Samu kari