Tsadar Mai
Duk da saukar farashi daga Dangote zuwa N875-N905, gidajen mai na sayar da man fetur a kan N890-N910, yayin da suke kukan asara saboda rage kudin da Dangote ke yi.
Gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da cewa ta ba mutane miliyan shida tallafin kudi cikin wata shida da suka gabata kuma akwai miliyan 15 da za su ci gajiya.
Dangote ya rage farashin fetur zuwa ₦825, inda gidajen mai na abokan hulɗarsa ke saida lita tsakanin ₦875 zuwa ₦905, ya danganta da yankin da mutane suke.
Ana fargabar jita-jitar mutuwa bayan cin wata shinkafa ya karya farashin kilo 50 zuwa N54,000 sakamakon rade-radin da ake yaɗawa da ya tayar da hankulan mutane.
Aliko Dangote ya kai ziyara NNPCL domin farfaɗo da haɗin gwiwa, bayan tangarɗar da aka samu a lokacin Mele Kyari, ana sa ran gina sabuwar alaka a tsakaninsu.
Peter Obi ya ce talauci na karuwa saboda gwamnatin Najeriya ta yi watsi da shugabanci, ya kuma bada gudummawar N40m domin lafiyar jama’a da ilimi.
’Yan kasuwa, karkashin kungiyar IPMAN sun ce yanzu asara suke yi bayan NNPCL da Dangote sun sauke farashin fetur, yayin da talakawa ke amfana da ragin a kasuwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana hasashen farashin man fetur zai sauka a Najeriya, biyo bayan faduwar farashin danyen man Brent a kasuwar duniya zuwa $65 a ganga.
NIPSS ta tabbatar da saukar farashin fetur kafin 2025, tana mai cewa aikin matatun Najeriya zai taimaka daidaita tattalin arziki da rage wahalhalun da ake fuskanta.
Tsadar Mai
Samu kari