Tsadar Mai
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su taya shugabanni da addu'a, kaunar juna, zaman lafiya, da hadin kai yayin bikin Kirsimeti na bana.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana kan yadda cire tallafin mai ya shafi mutane da tattalin arzikinsu inda ya ba da labarin yadda lamarin ya shafi wani abokinsa.
Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur inda ya ce babu nadamar da ya yi na daukar matakin a ranar 29 ga watan Mayu 2023 a Abuja.
Kamfanin NNPCL ya rage farashin fetur daga N1,020 zuwa N899 kan kowace lita, ana sa ran ƙarin ragin farashi kafin Janairu 2025 saboda faɗuwar farashin mai.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yara bakwai da wasu mutane uku yayin turereniya domin samun kayan tallafi saboda halin kunci a wani coci a Abuja.
A yayin da ake murnar Dangote ya rage farashin mai zuwa N899.50, su ma dillalai sun rage zuwa N939.50. Bincike ya nuna yadda gidajen mai suka fara canja farashin.
Matatar Dangote ta nemi NNPCL ta rika fadin labari yadda ya ya ke. Matatar na martani ne kan cewa ta ranci Dala biliyan daya domin ta fara gudanar da aiki.
Duba da halin kunci da aka sake shiga musamman a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara, Matatar man Aliko Dangote ta sake rage farashin mai.
NNPCL ya karbi bashin dala biliyan 1 don tallafawa matatar man Dangote, ya kuma jagoranci sake bude matatar Fatakwal da samun riba a karkashin Kyari.
Tsadar Mai
Samu kari