Labaran kasashen waje
Rahotanni daga Lebanon sun nuna cewa jirgin yaki mata matuki na Isra'ila ya afkawa musulmai bayan idar da sallah a wani masallaci a Kudancin Lebanon.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Antoni Janar ta kasar, Pam Bondi za ta sauka daga mukaminta ta koma bangaren kamfanoni masu zaman kansu.
Sojojin Isra'ila sun kakkabo makami mai linzami da aka harbo daga Yemen a yau, yayin da hare-haren Iran suka jikkata mutane a Kudus da sauran birane yau.
Yayin da ake ci gaba da musayar wuta a Gabas ta Tsakiya, Jamus ta roki China ta yi amfani da tasirinta ta lallaba Iran domin a kawo karshen wannan rikicin.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana cewa karfin soji ba zai iya warware matsalar shirin nukiliyar Iran ko bude mashigar ruwa ta Hormuz ba.
Hedkwatar rundunar sojojin Iran ta umarci manyan hafsoshi su kara sa ido kan yiwuwar shigar da dakarun makiya cikin kasar bayan barazanar Shugaba Donald Trump.
Kasashen da musulmi suka fi rinjaye ciki har da Saudiyya da Masar sun nuna adawada dokar hukuncin kisa da Isra'ila ta amince da ita kan Falasdinawa.
Dan Majalisa na jam'iyyar Democrat a Majalisar dokokin Amurka, Seth Moultonya caccaki Donald Trump kan yadda yake kokarin jefa rayuwar sojoji cikin hadari.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta tabbatar da cewa ta samu sako kan batun tsagaita wuta ta hannun masu shiga tsakani, ta ce za ta yi nazari a kai tukunna.
Labaran kasashen waje
Samu kari