Yan Kwallo
Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United ya bayyana kasar da ya ke so ta ci gasar AFCON da za a yi a yau Lahadi inda ya ce ya na goyon bayan Najeriya.
Hukumar kula da kwallon wasan nahiyar Afirika (CAF) ta sanar da cewa dan kasar Mauritania, Dahane Beida, ne zai hura wasan karshe tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire.
A ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu ya kamata a daura auren mataimakin Bursar na jami'ar jihar Kwara, Ayuba Olaitan, wanda ya rasu yayin kallon wasan Najeriya.
Wani ‘dan Najeriya wanda ya yi hasashen sakamakon AFCON a matakin rukuni, ya yi hasashen cewa Najeriya za ta yi nasara kan Ivory Coast a wasan karshe.
Wani ‘dan Najeriya ya ce zai fi kyautuwa mutum ya guji kallon wasan Najeriya da Ivory Coast idan har ya san yana da hawan jini. Ya ce zai fi kyau a bi sakamakon.
A yayin karo tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a wasan kusa da karshe na gasar cin kofin Afrika, AFCON, akalla ‘yan Najeriya biyar ne suka mutu saboda zullumi.
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya tuna haduwarsa da wani dan Obidient a yayin wasan Najeriya da Afrika ta Kudu.
A yau Laraba ce 7 ga watan Faburairu ne za a buga wasa tsakanin tawagar Najeriya ta Super Eagles da kasar Afirka ta Kudu a gasar AFCON a Ivory Coast.
Yayin da Najeriya ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe, an tattara bayanai kan kasar da za ta iya karawa da ita a wasan tsakanin Cape Verde ko Afrika ta Kudu.
Yan Kwallo
Samu kari