Yaki da cin hanci a Najeriya
EFCC ta mayar wa wata tsohuwa mai shekara 70, Margret Taye Odofin, N42.5m da jami’ar banki ta sace mata, bayan shekara da dama tana neman adalci.
Rundunar ‘Yan sanda ta janye karar Naira miliyan 400 da ta shigar kan tsohon Sanata Andy Uba da abokinsa, bayan sulhu tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da sauran wadanda ake tuhuma a kotu sun kawo tsaiko a zaman ranar Litinin.
Hukumar EFCC ta tabbatar cewa tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, na nan ƙarƙashin bincike duk da komawarsa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Gwamnatin Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da ‘ya’yansa guda biyu da wasu kotu bisa zargin almundahanar N4.4bn kan aikin tsandauri a Dala.
EFCC ta gurfanar da tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme, kan tuhumar karkatar da N1bn da dala miliyan biyu; sai dai Ngozi ta ki amincewa da wannan tuhuma.
Tsohon dan majalisar da ya wakilci Shanono/Bagwai a Kano, Hon. Farouk Lawan ya gode wa shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa afuwar da ya yi masa da wasu mutane.
Tashsar tsandaurin Dala ta fitar da rahoto kan zargin Abdullahi Ganduje da iyalansa da mallakar wani sashe na tashar da aka yi. Ta ce bita da kullin siyasa ne.
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta jihar Kano, PCACC ta fara binciken Abdullahi Umar Ganduje kan zargin badakalar Naira biliyan hudu a jihar.
Yaki da cin hanci a Najeriya
Samu kari