Ma'aikatar Ilimin Najeriya
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kawo tsarin bai wa dalibai lamunin karatu don inganta harkar ilimi a kasar, dalibai na dakon fara wannan shirin na ba da lamuni.
Shugaban Jami'ar Abuja, Farfesa Abdul-Rasheed Na'Allah ya bayyana cewa daga yanzu sai an yi wa dukkan dalibai gwajin kwayoyi kafin ba su gurbin karatu a Jami'ar.
Kungiyar Malaman Jami'o'i ta ASUU ta bayyana cewa dalibai da dama ka iya barin karatu idan har gwamnati ba ta dauki matakin kare-karen kudin makaranta da ta ke ba.
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ware makudan kudade don bai wa matasa masu bautar kasa musamman wadanda aka tura makarantu don farfado da ilimi.
Bayan zanga-zanga da ake ta yi a Najeriya kan kare-karen kudin makaranta, Jami'ar Legas ta rage kudin makarantar dalibai a yau Juma'a 15 ga watan Satumba.
Kotun majistare da ke zamanta a birnin Awka ta jihar Anambra ta daure lakcra, Peter Ekemezie kan zargin bata sunan Farfesa Asigbo na jami'ar UNIZIK da ke jihar.
Sabon ministan ilimi a gwamnatin Bola Tinubu, Farfesa Tahir Mamman, ya bayyana cewa zai yi aiki kamar magini a muƙamin da shugaban ƙasa ya ba shi. Ya bayyana.
Bola Tinubu bai yarda da zargin da ake yi wa gwamnati na rashin adalci a rabon Ministoci ba. Wasu su na zargin an bar Arewa da tarawa APC kuri'u a zabe kurum.
Hukumar ilmin ayyukan hannu (NBTE) ta ƙaddamar da shirin mayar da kwalin HND zuwa na digiri a Najeriya. Sabon shirin karatun zai kasance na tsawon shekara ɗaya.
Ma'aikatar Ilimin Najeriya
Samu kari