Babban kotun tarayya
Babbar kotun jiha dake zamanta a Kano ta bayar da umarnin a wallafa sammaci ga tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a manyan jaridun kasar nan biyu.
Yajin aikin da ƴan kwadago suka fara yau ya hana zaman sauraron ƙara game da rikicin masarautar Kano ranar Litinin, an ɗage zaman shari'ar har sai baba ta gani.
Kungiyar ma'aikatan kotu reshen birnin tarayya Abuja sun rufe manyan kotuna tare da hana alkalai, lauyoyi da masu shigar da kara aiki saboda yajin aikin NLC.
Babbar mai shari’a ta Kano, Dije Abdu Aboki ya ta bayyana cewa atsalandan a bangaren shari’a yana hana yanke hukunci da rashin gaskiya da adalci.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya sauya taken Najeriya, kungiyar lauyoyi ta ALDRAP ta shirya maka shugaban a kotu kan rashin bin tsari wurin tabbatar da dokar.
Wata kungiya mai rajin inganta harkokin shari'a a majalisa ta Association of Legislative Drafting and Advocacy Practitioners za ta maka shugaba Tinubu kotu.
Wata kotu dake zamanta a Koriya ta kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-young won tiriliyan 1.38.
Ikirarin cewa babbar kotun tarayya ta fi kowacce babbar kotun jiha karfin iko a wajen ba da umarni ba gaskiya ba ne. Lauya ya magantu kan rigimar masarautar Kano.
Kotun Koli ta umarci duka gwamnoni 36 da su yi martani kan zarginsu da Gwamnatin Tarayya ke yi game da dakile ƴancin ƙananan hukumomi 774 a fadin ƙasar.
Babban kotun tarayya
Samu kari