Nade-naden gwamnati
Farfesa Sulaiman Muhammad ya kare Isa Ali Pantami, yana cewa tarihin aikinsa da gudummawarsa ga tsaro sun cancanci a yi musu adalci tare da cikakken nazari.
Halima Shehu ta roƙi Tinubu ya umarci EFCC ta fitar da rahoton binciken da ta yi, tana cewa hakan zai wanke sunanta daga zarge-zargen da aka yi mata.
Bola Tinubu ya taya Ministan Ayyuka David Umahi murnar cika shekara 63, yana yabawa da ƙwazonsa tare da ƙarfafa shi ya ci gaba da ayyukan hanyoyi a Najeriya.
Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya sauke masu ba shi shawara na musamman takwas, tare da naɗa wasu tara sabbi, kwana biyu bayan sauke kwamishinoni shida.
Gwamna Abdullahi Sule ya amince da fatattakar kwamishinoni shida a Nasarawa, yana mai cewa sauyin wani bangare ne na dabarun kara inganta aikin gwamnati.
Isaac Fayose ya yi ikirari Bola Tinubu ya nada yayansa Ayo Fayose mukami ne kawai saboda ziyarar da Peter Obi ya kai masa kwanan nan, ya roki ya hakura da kujerar.
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabbin mutane 26 a hukumomin gwamnatin tarayya guda 10, inda Ayo Fayose da Junaid Bindawa suka samu manyan mukamai a sabbin naɗe-naɗen
Yayin da ake tunkarar 2027, Gwamna Inuwa Yahaya ya rantsar da kwamishinoni 23 a Gombe, ya bukace su su fara aiki nan take tare da gujewa cin hanci da rashawa.
Rikici ya ɓarke kan shugabancin BCDA bayan an ce Dr Abdulrazak Namdas bai karɓi takardar naɗinsa ba duk da sanarwar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Nade-naden gwamnati
Samu kari