Nade-naden gwamnati
Hadimij shugaban Najeriya, Daniel Bwala ya ce kafar Al Jazeera ta ba shi hakuri a asirce kan hirarsa da Mehdi Hasan, amma ta ki fitar wa a bainar jama'a.
Shugaban hukumar PFIPC da ake takaddama a kanta, Adeniyi Adeyemi Matthew, ya bayyana dalilin da ya sanya ya kafa hukumar. Ya ce domin jawo masu zuba jari ne.
A labarin nan, za a ji cewa gwamantin Bola Ahmed Tinubu ta fito da bayanai kan zargin hukumar bogi da aka kafa a karkashinta na da asusu a bankin CBN a kasar nan.
Gwamna Bala Mohammed ya yi alhinin rasuwar tsohon Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza, wanda ya rasu a Abuja bayan doguwar jinya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta bada umarnin gudanar da bincike kan hukumar PFIPC.
Mai ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya yi zarge-zarge kan gwamnatin tarayya. Adeniyi ya ce gwamnati na kokarin rufe masa baki.
Prince Adeniyi Adeyemi ya dage cewa nadin da aka ba shi na shugaban wata hukuma ta gaskiya ne duk da zargin jabun takardu da rike mukamin da ya ke yi.
Wata ƙungiyar fararen hula ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin lafiya tare da sauke Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate.
Fadar shugaban kasa ta zargi Adeniyi Adeyemi da kafa ma'aikatar bogi a Najeriya ba tare da sanin shugaban kasa Bola Tinubu da sauran hukumomin Najeriya ba.
Nade-naden gwamnati
Samu kari