Nade-naden gwamnati
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da nadin dan uwan Abubakar Malami (SAN) a matsayin shugaban hukumar KEBGIS bayan ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya fatattaki masu bashi shawara na musamman har su 30 domin sake tsara gwamnati da karfafa ajandar 'sabuwar Neja'.
Aisha Buhari ta bayyana dalilan da suka sa marigayi Muhammadu Buhari bai cika sallamar ministoci da hadiman gwamnatinsa. Ta fadi kura-kuran tsohon shugaban.
Majalisar dattawa ta fara tantance sunayen jakadu da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa mata, inda ta tantance mutum mutum 3 da suka fuskanci tuhume-tuhume.
Kotu a Abuja ta umarci a tsare tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, a Kuje kan tuhumar rashawa da almundahana. Za a saurari bukatar belinsa a ranar Litinin.
An bayyana yadda EFCC ta kama Dr. Chris Ngige a gidansa da daren Talata, inda aka tafi da shi cikin kayan barci, kuma ake zargin za a gurfanar da shi kotu yau.
Gwamna Baba Kabir Yusuf ya amince da nadin Farfesa Amina Salihi Bayero a matsayin shugabar jami'ar Northwest ta Kano bayan ta cika sharuddan tantancewa.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin waje ya nuna damuwa kan yadda wanda aka nada ya gaza kiran duka sunayen sanatocin da suka fito daga jiharsa.
Julius Bokoru ya zargi EFCC da karya doka bayan ta zana “EFCC—Keep Off” a gidan tsohon minista Timipre Sylva, yana cewa an rufe gidan ba tare da wata sanarwa ba.
Nade-naden gwamnati
Samu kari