Yan bindiga
Rundunar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta tono gawar yan banga da aka yiwa kisan gilla aka birne su. Yan sanda sun kama mutane biyar da wani basarake kan laifin.
Gwamnatin jihar Neja ta fara tuntiɓar rundunar sojojin Najeriya domin duba yiwuwar sake buɗe sansanin sojoji a Alawa biyo bayan harin da aka kai kwanan nan.
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin rundunar MNJTF sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin su ke safarar miyagun kwayoyi ga Boko Haram da ISWAP.
Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra inda suka kewaye sakatariyar karamar hukuma suka cinna wuta da harbe harbe kafin yan sanda su zo.
Yan ta'adda da ake zargin yan Boko haram ne sun kai hari makarantar Faudiyya mallakin yan Shi'a a jihar Yobe. Boko Haram ta harbe yan Shi'a uku da jikkata daya.
Yan bindiga sun kai hari yankin Ushafa da ke Bwari a birnin tarayya Abuja inda suka kashe magidanci da sace matar aure da yara. Yan bindigar sun kai harin ne da dare
Mutanen gari a ƙauyen Matusgi da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara sun yi fito na fito da 'yan bindiga. Sun hallaka mutum 37 har lahira.
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja ya kwantarwa al'umma hankulansu game rashin tsaro inda ya ce saura kiris a gama da matsalar.
Yan bindiga sun kai hari kan tsohon dan sanda kuma jagoran tsaro a wani kauye inda ya tsallake rijiya ta baya. Sun bude wuta ga motarsa kafin su cinna mata wuta.
Yan bindiga
Samu kari