Yan bindiga
Matar Janar Rabe Abubakar da ya mutu a hannun masu garkuwa da mutane ta ki tafiyaa lokacin da 'yan bindiga suka ce ta tafi.'Yar Janar Rabe ta fadi me ya faru a daji.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce matsalar tsaron Najeriya bata kai yadda mutane ke yawan fadan ta ba. Ya ce mutane na ruruta matsalar tsaro.
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nada tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, a matsayin wakilin jihar a Asusun Tsaron Arewacin Najeriya.
Gwamnatin Jihar Oyo ta ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 16 a kananan hukumomi 10 da ke makwabtaka da tsohuwar gandun dabbobi domin magance matsalolin tsaro.
Tsohon shugaban APC na Koko/Besse a jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Besse, ya rasu a hannun ‘yan bindiga bayan an sace shi a farkon watan Yunin 2026.
'Yan bindiga sun sace iyalan shugaban APC na karamar hukumar Yauri a jihar Kebbi, Alhaji Yusuf Alhassan. An sace matar shi da dan shugaban APC a Kebbi.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani hari a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun farmaki manoman da ke aiki a gona inda suka kashe wasu daga cikinsu.
Dakarun sojojin Najeriya sun kai wani samame a maboyar 'yan ta'adda da ke jihar Katsina. Sojojin sun hallaka 'yan ta'adda tare da kwato manyan makamai.
Dakarun Najeriya sun kashe 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna bayan wani farmaki da suka kai. Sojojin sun yi nasarar cafke mutane huɗu a Kaduna.
Yan bindiga
Samu kari